DON DAWO DA MARTABAR NONO DA GIRMANSA
DON DAWO DA MARTABAR NONO DA GIRMANSA
Wannan wani hadine da akeyi don gyaran nono musamman ga budurwa, shi wanna hadi kuma kowace mace inda tana da bukata zata Iya amfani dashi saboda tasirinsa, yanda akeyi shine.
Garin waken soya
Garin alkama
Garin zogale
Garin bawon lemun Zaki
Kunfan maliya
Zuma
Sai ki cakudasu guri daya sai ki rinka shafawa a nonon bayan minti 30 ko sama da haka sai a wanke, sannan kuma ki rinka shan kunun alkama.
DON DAWO DA MARTABAR NONO DA GIRMANSA
Ga matar da take son ta dawo da martabar nononta ko girmansa yanda zatayi shine zata Samu:
Ganyen sabara
Ya’yan alkama
Sai ki rinka yin kunu dasu kamar haka
Kunun alkama
Kunun shinkafa
Kunun gero
Kunun waken soya
Duk Wanda yasamu sai ki dafashi da wadannan hadin mai albarka, kuma kina Iya saka cokali Biyu na ya’yan hulba sai ki rinka shansa karamin ludayi sau biyu a Rana safe da gamma kenan.
DON FARFADO DA NONON DA YA NOKE YA SHAFE
Idan nononki ya noke ya shafe to ga hanyar da zaki bi don farfado dashi ko dawowa dashi cikin sauki.
Ya’yan alkama
Ya’yan hulba
Raihan kamar cokali biyu
Sai ki rinka dafa shayi dasu da Zuma sai ki ringa shan cokali uku safe uku yamma , sannan kuma ki rinka shafe nonon naki da man zaitun.
KARIN GIRMAN NONO
Ganyen tatarida.
Wake.
Gurjiya.
Alkama.
Ki samu wake gwangwani daya gujiya gwangwani Biyu, alkama gwangwani Biyu ki Kai inji a nika miki, ki daka ganyen tatarida gari gwangwani daya ki hada, guri guda ki dinga zubawa a nono kindirmo Mara tsami kina sha, Amma garin magani cokali biyu nono kamar na naira 40
Comments
Post a Comment