Zuwaga Masu Matsalar Rashin Haihuwa
Zuwaga Masu Matsalar Rashin Haihuwa
Rashin haihuwa babbar matsalace indai Allah Bai bakaba, Amma yawanci akwai abubuwan Dake haddasasu.
Zamu tattauna akan bubuwan dake haddasa matsalar zuwa hanyoyin da zaa magancesu.
1.Wajibine asani ita haihuwa lamarine daga ubangiji shike bayarwa ga wanda yaso akuma lokacin da yaso.
2.Fitar farin ruwa ga mace ko namiji ta sanadiyar kamuwa da ciwon sanyi, shima kan hana samuwar ciki.
3.Haka ma karin mahaifa wato (fibroids) shima na hana samuwar ciki.
4.Masana aharkar iyali sun bayyana cewa sai maniyyin namiji yakai tsawon kwana 3 wato kimanin 72 hours sannan ya zamana zai iya samar da ciki,Shiyasa ko gwajin za'a yiwa mutum na test akan kwayoyin halittar to sai maniyyin Da yayi kwana uku sannan su iya ganewa.
Don haka sai akiyaye da kuma tabbatar da ansamu kwanakin nan sannan asadu, musamman agab da mace zatayi al'ada da kwanaki 3 ko kwanaki 4 zuwa 5 bayan Al'ada.
5.Kuma Yana da kyau mace ta daina saurin tashi bayan gama jima'i domin maniyyin yasamu damar gangarawa cikin jikinta musamman cikin mahaifa. Haka kuma kafin mace ta fara al'ada da kwanaki wasu Matan alokacin suke fitar da kwayayen halittarsu inda zasu jira haduwar maniyyin namiji ta yadda zasu gangara mahaifarta.
6.Sannan akwai tsari na ubangiji inda za'a samu wani bai da matsala itama matar lokaci ne dai bai yiba.
7.Ba wai ruwan da ake gani shine maniyi ba. shi semen ake kiranshi. kaurinshi ko rashin kaurinshi bai da nasaba da hana haihuwa. matukar akwai isasshen kwayoyin maniyin a cikinsa.Shi kwayoyin maniyi sai da microcope ake ganinsu kuma zaka gansu kamar yayan gwadari ne suna yawo a cikin semen din kuma daga yan kwadu suke fitowa su biyo ta vas deferense su hadu da semen din sannan su shiga cikin mahaifa in anyi jimai.
lallai karancin maniyi yana hana haihuwa domin sai yawan kirgan 'ya'yan maniyin yakai miliyan arbain kafin ya iya ma mace ciki shi yasa ake sperm count daga karshe a gano Mutum yanada low sperm count.
Comments
Post a Comment