Dukkan Nau'ikan Lalurar sanyi na Mata.

 Dukkan Nau'ikan Lalurar sanyi na Mata.



Kaikayin gaba

Kurajen gaba

Fitar farin ruwa

Daukewar Sha'awa

Gushewar Ni’ima

Kullewar mara

Ciwon baya

Fitsarin jini

Fitsari Mai fita da zafi

Warin Gaba

Da sauran su


To duk mace Mai fama da 1 daga cikin wannan lalurar to ga yadda zatayi Nan saita Sami wadannan ta hada

Garin bagaruwa cokali 3

Kanwa cokali 2

Gishiri cokali 1

Tafarnuwa kunso 1


Azuba ruwa daidai yadda za iya shiga azauna, sai atafasa sosai idan a gas ne to minti 30 zaiyi,inko a itace ne to awa 1 Zaki barshi yayi. Amma tafarnuwa a daka ta ko agoge ta.



Bayan kinyi wannan sai  atsiyaye, atace azauna ciki na tsawon minti 15 Amma fa da dumi ba da zafi ba.


Bayan wannan Sai kuma Asami man zaitun

Man tafarnuwa

Man kwakwa

Tafarnuwa

Sai atoyasu ayanyanka tafarnuwa aciki.

Daganan sai kisami audiga adangwali man ayi matsi ba za acire ba sai bukatar Hakan ta taso.


Hadin Wanda za'a Sha,kisami

Kankana na 100

Tsamiya sili 4

Tafarnuwa kunso 1 babba

Turmeric (kurkur) guda 4

Jar Albasa Rabi

Citta gada 1

Ruwa pure water 6


Zaki soatafasa sosai kana atsiyayeshi atace arinka Sha. AMMA FA Wannan hadin Banda Mace Mai ciki ko Mai shayarwa ko kankanin yaro duk basa Sha.


Mace Mai ciki ga nata

Kisami

Kankana na 100

Tsamiya sili 4 Amma fa sabowar ba tsohuwar ba

Tafarnuwa kunso 1

Shima za'a hada ne a tafasasu sai arinka Sha.


Allah yakara lafiya yasa mudace

Comments