DON DAWO DA MARTABAR NONO DA GIRMANSA
DON DAWO DA MARTABAR NONO DA GIRMANSA Wannan wani hadine da akeyi don gyaran nono musamman ga budurwa, shi wanna hadi kuma kowace mace inda tana da bukata zata Iya amfani dashi saboda tasirinsa, yanda akeyi shine. Garin waken soya Garin alkama Garin zogale Garin bawon lemun Zaki Kunfan maliya Zuma Sai ki cakudasu guri daya sai ki rinka shafawa a nonon bayan minti 30 ko sama da haka sai a wanke, sannan kuma ki rinka shan kunun alkama. DON DAWO DA MARTABAR NONO DA GIRMANSA Ga matar da take son ta dawo da martabar nononta ko girmansa yanda zatayi shine zata Samu: Ganyen sabara Ya’yan alkama Sai ki rinka yin kunu dasu kamar haka Kunun alkama Kunun shinkafa Kunun gero Kunun waken soya Duk Wanda yasamu sai ki dafashi da wadannan hadin mai albarka, kuma kina Iya saka cokali Biyu na ya’yan hulba sai ki rinka shansa karamin ludayi sau biyu a Rana safe da gamma kenan. DON FARFADO DA NONON DA YA NOKE YA SHAFE Idan nononki ya noke ya shafe to ga hanyar da zaki bi don farfado dashi ko dawowa das